Shaikh Muhammad Awal ya kira 'yan Najeriya suyi koyi zamantakewar dake tsakaini mutanen Amurka

Shaikh Muhammad Awal ya kira 'yan Najeriya suyi koyi zamantakewar dake tsakaini mutanen Amurka

- Shaikh Muhammad Awal mazaunan kasar Amurka ya bukaci ‘yan Najeria cewa ya kamata a zauna da juna lafiya

- Malamin ya ce ‘yan Najeriya suyi koyi da zamantakewar dake tsakanin mabiya addinai daban daban a kasar Amurka domin ciyar da Najeriya gaba

- Babban malamin ya kara da cewa Allah ya albarkaci kasar Najeriya da kabilu daban daban da addinai da yawa

Shaikh Muhammad Awal malamin addinin Islama kuma dan asalin Najeriya dake zaune a Amurka ya bada lecca albarkacin watan ramadan a birnin Legas inda ya kira musulmai da wadanda ba musulmai ba a Najeriya da suyi koyi da zamantakewar dake tsakanin mabiya addinai daban daban a kasar Amurka domin ciyar da Najeriya gaba kamar yadda tsarin Islama ya tanada.

Inji Shaikh Awal kowa ya san matsayin Amurka da musulunci da sauran addinai. Ya ce akwai mutanen kirki da yawa a Amurka haka kuma akwai miyagun mutane. Malamin ya kara da cewa suna da 'yanci su gina masallatai tare da walwalar gudanar da addininsu.

Yace lokacin da shugaban Amurka ya ayyana dokar hana musulmai daga wasu kasashe shigowa kasar Amurkawa suka yiwa musulmai kariya suyi sallar juma'a a duk filayen jiragen sama na manyan birane.

KU KARANTA: To fa! Kasar Saudiyyah ta hana 'yan Qatar yin aikin Umrah

Yana mai cewa zamantakewar mutane ta hanyar nuna soyayya da taimako shi zai jawo hankalin mutane cikin musulunci saboda haka Annabi Muhammad (SAW) ya zauna a Mecca da Medina.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, malamin ya ce Allah ya kirkiro Najeriya da kabilu daban daban da addinai da yawa da harsuna ga kuma albarka da yaba kasar. Saboda haka 'yan Najeriya su nemi hanyar zaman lafiya da juna domin su samu cigaban kasar baki daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus da cocin Living Faith Church

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel