'Dole fa kabilar Ibo su bar Arewa a wa'adin da muka deba musu'

'Dole fa kabilar Ibo su bar Arewa a wa'adin da muka deba musu'

- Hira da wadanda suke barazanar korar kabilar Ibo daga arewa sunce yana nan daram

- Ga dukkan alamu dai ba'a kame samarin ba, kamar yadda hukumomi suke ta kwakwazo

- Tuni wasu kabilun ma sun fara koma wa gida, daga bangarorin kasar

A hira da jaridar vanguard, sakataren kungiyar samari na arewa, Alh. Ahmed Sule, yace dole ne abi tsarin da suka kasa na cewa sai kabilar Ibo sun bar kasar arewa saboda arewar, a cewarsa, ta gaji da cin kashi da 'yan kabilar Ibo ke yi wa arewar.

Ya ce: "mun zauna lafiya da su, amma kullum sai kaji zancen su baya wuce Biyafara, sun ce mana jahilai, sun ce mana 'yan ta'adda, da dai kalamai na banza, amma mu bama tanka musu."

Ya kara da cewa: "mu ba fada muke ba, kuma ba wai fada zamu yi ba, a'a, kawai dai tunda suna son ayi sakin aure tsakanin kabilun kasar nan, to su ja nasu ya nasu su tafi."

Dole fa kabilar Ibo su bar Arewa a wa'adin da muka deba musu'

Dole fa kabilar Ibo su bar Arewa a wa'adin da muka deba musu'

An dai sami tarnaki sosai bayan da samarin suka fitar da sanarwa a makon jiya kan lallai sun baiwa kabiloun kudu watannin uku su tattara kayansu su tafi kudu.

KU KARANTA KUMA: Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - JegaBai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

An dai bafda sammacin a kama su, amma ga dukkan alamu ma kara goyon baya suke samu daga wasu da suke kiran kansu dattijan arewa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon hiran shugaban Biyafara Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel