An baiwa wasu shugabannin Yarbawa cin hanci domin su boye wadanda suka kashe Abiola – Manjo Al-Mustapha

An baiwa wasu shugabannin Yarbawa cin hanci domin su boye wadanda suka kashe Abiola – Manjo Al-Mustapha

-Al- Mustafa ya fasa kwai akan shugabannin yankin Yarbawa kan mutuwan Abiola

-Ya ce lallai yanada hujja kan kalamansa

Tsohon hafsan tsaron tsohon shugaban kasa Sani Abacha. Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa an bawa wasu shugabannin kabilar Yoruba cin hanci domin boye wadanda suka hallaka Cif MKO Abiola.

Yace shugabannin Yarbawa sun sani kwarai wanda ya kashe Abiola amma sukayi shiru kma mushirkai saboda an toshe musu baki da cin hanci.

An baiwa wasu shugabannin Yarbawa cin hanci domin su boye wadanda suka kashe Abiola – Manjo Al-Mustapha

Manjo Al-Mustapha

Al Mustapha yayi wannan bayani ne yayind yake amsa tambayoyin yan jarida a jihar Kaduna jiya inda yace yanada hujjan bidiyo na abubuwan da ya faru a fadar shugaban kasa da sarakunan Yarbawa.

KU KARANTA: Ana cigaba da kokarin tsige Dino Melaye

Yace kwana daya bayan mutuwan Abiola, "wani shugaban yankin Yarbawa ya shigo fadar shugaban kasa tare da abokansa. Ya shigo Villa a fusace. A lokacin sun zo yakan gwamnati ne amma da suka fito daga ganawar, suka dinga sheka dariya tamkar babu abin da ya faru a kasar. Anyi safara kudi kuma sun basar da Abiola.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel