YANZU YANZU: Majalisar wakilai na ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro

YANZU YANZU: Majalisar wakilai na ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro

- Yan majalisa na cikin ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro

- Zasu gana ne a kan al'amarin sace-sacen mutane da ya yawaita a kasar

Mambobin majalisar wakilai na cikin ganawar sirri tare da ministan tsaro da ministan cikin gida da kuma shugabannin hukumomin tsaro kan yawan sace-sacen mutane da ake fama da shi a kasar.

Har ila yau sauran wadanda suka galarci taron sun hada da sufeto janar nay an sanda, Ibrahim Idris, da kuma darakta janar na hukumar yan sandan sirri Lawal Daura.

KU KARANTA KUMA: Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

A ranar Alhamis da ya gabata ne ne majalisa ta aiaka sammaci gare su, harma da mai ba kasa shawara a harkar tsaro Babagana Monguno don suyi jawabi ga yan majalisa a yau.

YANZU YANZU: Majalisar wakilai na ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro tsaro

Majalisar wakilai na ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro tsaro

Ana sa ran manyan shugabannin tsaro zasuyi bayani kan dalilin da yasa ake samun yawan sace-sacen mutane musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suke sace mutane a kullun sannan kuma su karbi miliyoyin naira a matsayin kudin fansa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan ko mutane sun dauki yan sanda abokai.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel