An kammala biyan kudaden tallafi zagaye na farko a Bauchi, an soma kashi na biyu

An kammala biyan kudaden tallafi zagaye na farko a Bauchi, an soma kashi na biyu

- Gwamnatin tarayya ta kammala biyan kudaden tallafi zagaye na farko ga al’mmar jihar Bauchi

- Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar cewa kamfanin FETS LTD dake da alhakin tura kudaden tallafin ta soma zagaye na biyu

- Gwamnatin jihar Bauchi ta ci gaba da cewa za ta zuba kimanin biliyan 1.31 a cikin tattalin arzikin jihar

Gwamnatin tarayya ta biya zagayen farko na naira miliyan 103 kudaden tallafi ga mutane 10,312 a karkashin shirin tallafin dubu biyar biyar a jihar Bauchi,

Kudaden suna matsayin tallafin watan Disambar 2016 da watan Janairun 2017.

Bayanin hakan ya fito ne daga mai taimakawa gwamnan Bauchi a fannin harkokin kungiyoyi Mansur Manu Soro a yayin ganawarsa da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati na jihar Bauchi wanda kuma shine shugaban hukumar rage radadi ta jihar da wakilan kamfanin FETS Ltd.

A sanarwar hadimin gwamnan jihar Bauchi a fannin sadarwa, Shamsudeen Lukman ya fitar ya ce tun a ranar 9 ga watan Yunin da muke ciki kamfanin FETS LTD dake da alhakin tura kudaden ya soma zagaye na biyu na shirin a inda ya fara biyan kudaden tallafi na watan Fabairu da Maris 2017.

KU KARANTA: Gwamnatinmu ta jama'a ce - inji wani gwamnan arewa

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Shamsudeen ya ce gwamnatin jihar ta kuduri aniyar zuba kimanin Biliyan 1.31 a cikin tattalin arzikin jihar ta hanyar amfani da fasahar tura kudi ta zamani nan da watanni 24 masu zuwa.

Yana mai cewa gwamnatin jihar Bauchi zata ci gaba da hada guiwa da gwamnatin tarayya domin rage radadin da talakawan jihar ke fama dashi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun na tukar uwargidansa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel