EFCC ta shiga bincike akan badakalar kasafin kudin 2016, ta gayyaci Jibrin

EFCC ta shiga bincike akan badakalar kasafin kudin 2016, ta gayyaci Jibrin

- Hukumarb EFCC ta gayyaci Abdulmumin Jibrin

- Ta gayyace shi ne don ya bata karoin haske a kan badakalar da ya ce an aikata a kasafin kudin 2016

- Gayyatan na zuwa ne bayan wasu abubuwa da hukumar ta gano

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta gayyaci dakataccen dan majalisar wakilan nan Abdulmuminu Jibrin domin ya zo ya yi mata karin haske game da korafin da ya shigar mata akan badakalar da ya ce an aikata a kan kasafin kudin 2016.

Takardar gayyatar mai dauke da kwanan wata 9 ga watan Yuni ta bayyana cewa hukumar tuni ta shiga bincike game da korafe korafen cin hanci da rashawa da dan majalisar ya yi.

Ta kara da cewa a sakamakon wasu abubuwa da hukumar ta gano a baya bayan nan, ya zama wajibi ta gayyaci shi domin ya yi mata karin haske.

EFCC ta shiga bincike akan badakalar kasafin kudin 2016, ta gayyaci Jibrin

EFCC ta shiga bincike akan badakalar kasafin kudin 2016, ta gayyaci Jibrin

An bukaci Jibrin da ya ziyarci ofishin hukumar da ke lamba 5 a kan titin Fomelu a Wuse 2, Abuja, a yau Talata da misalin karfe 10 na safe.

KU KARANTA KUMA: Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - JegaBai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

A wata takarda da ya fitar ga manema labarai, Abdulmuminu Jibrin ya ce ya ji dadin wannan gayyata, saboda ta zo ne a dai dai lokacin da mutane da dama suka hakura da fatan cewa za a dauki mataki akan korafe korafen.

Ya ce sau da yawa, ya sha fadin cewa ya yi imani da gaskiyar hukumar EFCC a karkashin shugabancin Ibrahim Magu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyo wanda ke tambaya a kan cewa ko sabon jam'iyyar siyasa ne maganin matsalar Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel