To fa! Kasar Saudiyyah ta hana 'yan Qatar yin aikin Umrah

To fa! Kasar Saudiyyah ta hana 'yan Qatar yin aikin Umrah

Sakamakon yanke alakar da Saudiyya tare da wasu kasashen da gwamnatin Qatar, mahukuntan Saudiyya sun hana wasu 'yan kasar Qatar gudanar da aikin Umrah.

Jaridar Al-Sharq ta kasar Qatar ta bayar da rahoton cewa, shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na kasar Qatar Ali bin Sumaikh Al-Marriya bayyana cewa, 'yan kasar Qatar da ke zaune a Saudiyya da kuma wadanda suka je aikin Umrah suna fuskantar cin zarafi daga mahukuntan Saudiyya inda ake hana su shiga cikin masallacin haramin Makka domin gudanar da ibada.

NAIJ.com ta samu labarin cewa jami'in ya ce kwamitinsa ya samu korafi irin wannan ya kai kimanin 700 a cikin kasa da kwanaki 5 da suka gabata.

To fa! Kasar Saudiyyah ta hana 'yan Qatar yin aikin Umrah

To fa! Kasar Saudiyyah ta hana 'yan Qatar yin aikin Umrah

Saudiyya da da wasu kasashen larabawa da take dasawa da su da kuma wasu kasashen da take bai wa taimakon kudade a Afirka, sun sanar da yanke alaka da Qatar saboda zarginta da taimaka wasu kungiyoyi da suka kira na 'yan ta'adda, da suka hada da Hamas da kuma kungiyar 'yan uwa musulmi mai mazauni a kasar Masar.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel