Babban dalili 1 tak da ya sa muka haramta tashe a jihar Kano - Yan sanda

Babban dalili 1 tak da ya sa muka haramta tashe a jihar Kano - Yan sanda

- Tashe wasannin al`ada ne da ake yi a cikin watan azumi, musamman ma daga goma sha biyar ga wata. inda maza da mata, yara da matasa ne ke bin gida-gida dan yin wasan tashe, don debe kewa ga masu azumi a duk shekara.

- Sai dai, a bana mahukunta a Kano sun hana yin wasan tashe saboda dalilai na tsaro, lamarin da ya rage armashin hidimomin da ake yi a cikin watan azumin.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya, ya ce an dauki matakin ne saboda dalilai na tsaro yawancin lokuta bata gari kan saje cikin masu tashe dan aiwatar da ayyukansu.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Sarki Na-Lako Awwalu Sani wato Sarkin Gwagwaren Kano, kuma shugaban masu tashe , wanda za a iya cewa wasansa ne kolin wasannin tashe a Kano, musamman ranar kamun gwagwar, ya shaida wa BBC cewa za su yi biyayya ga matakin da gwamnati ta dauka.

Babban dalili 1 tak da ya sa muka haramta tashe a jihar Kano - Yan sanda

Babban dalili 1 tak da ya sa muka haramta tashe a jihar Kano - Yan sanda

Hana wasan tashe ya tada hankalin mutane da dama, ciki har da ma`abota nazarin harshe da al`adun Hausawa, wadannan ke kallon matakin a matsayin wani yunkuri na kashe wasan tashe tare da yin illa ga fagen nazari, kasancewarsa daya daga cikin wasannnin da ake nazarinsu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel