Fayose ya bukaci gwamnatin tarayya ta sasanta ‘yan Arewa da kabilar Igbo

Fayose ya bukaci gwamnatin tarayya ta sasanta ‘yan Arewa da kabilar Igbo

- Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayoshe ya bukaci gwamnatin tarayya ta sasanta ‘yan Arewa da kabilar Igbo

- Gwamnan Ya ce yanzu kasar Najeriya tafi rarrabuwa a cikin shekaru 2 da suka wuce

- Fayose Yace ko a turai ana samun irin wadannan matsaloli tsakanin kabilun kasar

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayoshe ya ce lamarin abin takaici ne, bashi cikin ra’ayin kasar mu irin haka ya rika faruwa. Yace idan aka duba za’a ga cewa kasar Najeriya tafi rarrabuwa a cikin shekaru 2 da suka wuce, kuma wannan ba shine shugabanni irin su marigayi Tafawa Balewa da Dakta Nnamdi Azikiwe da Cif Obafemi Awolowo suke son gani ba.

A kan batun ballewar kabilar Igbo daga Najeriya, gwamna Fayoshe yace: “wannan ba ra’ayin shugabanni mu na farko bane, amma ina son gwamnatin tarayya ta zama uba ga kowa, a saurare kowa a yi sulhu, saboda sulhu itace hanya mafi kyau na shawo kan kowace matsala. Zaman dardar ya yi yawa a Najeriya, ya kamata a zauna da al’umman Igbo a tattauna da su.”

KU KARANTA: Biafra: Bamu goyon bayan Nnamdi Kanu, garambawul kawai muke so – Ohanaeze Ndigbo

Fayose ya bukaci gwamnatin tarayya ta sasanta ‘yan Arewa da kabilar Igbo

'Yan kabilar Igbo masu fafutukar neman yankin Biyafara

Da ya ci gaba da bayani, gwamnar na jihar Ekiti ya ce yana nufin Najeriya ta kasance kasa daya. Yace ko a turai ana samun irin wadannan matsaloli, yayi misali da Northern Ireland da Britaniya, amma hanyar magance su sune a zauna ayi sulhu.

Yace a saurari kowa, gwamnatin tarayya ta kula da kowa. Gwamna Ayodele Fayoshe yace mafita itace gwamnatin Najeriya ta canza dabi’unta, Najeriya kasa ce mai kabilu da yawa kada a yi amfani da karfi a rufe bakin wasu jama’a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shekaru 50 da fara fafutukar kafa kasar Biyafara, shin 'yan kabilar Igbo za su iya cimma burinsu kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel