‘Yan sanda sun ba ‘yan kabilar Igbo mazauna Kano tabbacin samun kariya da ya dace

‘Yan sanda sun ba ‘yan kabilar Igbo mazauna Kano tabbacin samun kariya da ya dace

- Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Rabi’u Yusuf, ya ba ‘yan Igbo mazauna jihar tabbacin samun kariya daga su har dukiyoyinsu

- Hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta yi kira ga ‘yan Igbo mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu sannan kuma su ci gaba da gudanar da al’amuransu bisa doka.

- Sarkin Igbo na Kano, Boniface Ibekwe ya bukaci ‘yan Igbo mazauna jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da tsoron ko wani cin zarafi ba.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Rabi’u Yusuf, ya ba ‘yan Igbo mazauna jihar tabbacin samun kariya daga su har dukiyoyinsu.

Wannan na dauke ne a cikin wani jawabi da jami’in hulda da jama’a Magaji Majiya,ya saki a Kano a ranar Talata 13 ga watan Yuni, kamfanin dilancin labarai na Najeriya (NAN) ta rahoto.

Mista Yusuf ya bayar da tabbacin ne a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni a gurin wani taro da shugabannin al’umman Igbo na jihar.

KU KARANTA KUMA: An tsaga da rabo: Yadda Sanata Dino Melaye ya sha da kyar

NAIJ.com ta tattaro cewa a nashi bangaren, sarkin Igbo na Kano, Boniface Ibekwe ya nuna godiyarsa ga kwamishinan kan kiran taron a lokaci mai muhimmanci”.

Mista Ibekwe ya yaba wa mutanen jihar Kano, cewa suna da hali na gari da kuma juriya a kan sauran kabilu dake tsakaninsu.

Ya kuma yi kira ga dukkan ‘yan kabilar Igbo a jihar da su kwantar da hankulansu kamar yadda har yanzu Kano jihar su ne tunda a nan suka haifi yawancin ‘ya’yansu.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bayan shekaru 50 kuna ganin za'a cimma Biyafara kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel