ASARA! Ya fadi ya mutu don an doke kungiyar kwallon kafar Najeriya

ASARA! Ya fadi ya mutu don an doke kungiyar kwallon kafar Najeriya

- Wani tsohon sojan Nijeriya da aka bayyana sunasa da Joseph Oloruntoju ya fadi ya mutu har lahira a ranar Asabar din da ta gabata bayan da tawagar Afurka ta Kudu, Bafana Bafana ta lallasa tawagar Nijeriya, Super Eagles a garin Uyo babban birni jihar Akwa Ibom

- Super Eagles ta Nijeriya ta sha kashi a hannun takwararta ta Bafana Bafana a wasan share fagen shiga gasar cin kofin Afurka

Oloruntoju wanda tsohon soja ne da ya yi ritaya a matsayin sajan ya bar gidansa da ke unguwar Ajipowo da ke garin Akure zuwa barikin sojoji na Owena domoin kallon fafatawar cikin abokansa.

Wata majiya ta bayyana Oloruntoju ya bayyana a matsayin cikakken masoyin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya wanda hakan ne ma ya sanya ya fadi magashiyan bayan tawagar Afurka ta Kudu ta zura kwallo ta biyu a ragar Nijeriya.

ASARA! Ya fadi ya mutu don an doke kungiyar kwallon kafar Najeriya

ASARA! Ya fadi ya mutu don an doke kungiyar kwallon kafar Najeriya

NAIJ.com ta samu labarin cewa wadanda ke wajen sun gaggauta kai shi wani asibiti mai zaman kansa mafi kusa, inda a nan ne aka tabbatar da mutuwarsa.

Jami’in hulda da jama’a na runduna ta 32 na sojin Nijeriya da ke Akure, Kyaftin Ojo Adelegan ya tabbatar da labarin, inda a nasa rahoton ya bayyana cewa tsohon sojan ya fadi ne a cikin barikinmu amma ba lokacin da ya ke kallon kwallon kafa ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel