Gwamnati ta hambare shirin majalisar dattijai kan kirkirar wasu sabbin hukumomi

Gwamnati ta hambare shirin majalisar dattijai kan kirkirar wasu sabbin hukumomi

- A tsarin gwamnati ba dai-dai bane a sami hukumomi masu aiki iri daya

- Ana samun takun saqa tsakanin gwamnatoci da majalisunsu

- Antoni Janar na kasa yayi fatali da kudurin hukuma

A kokarin gwamnatin tarayya na rage yawan ma'aikatu masu aiki iri daya da juna, antoni janar na kasa Abubakar Malami, ya hambare kudurin majalisar dattijan kasar nan don samar da sabbin hukumomi da aikinsu ke kama da na ma'aikatar sharia ta kasa.

Kudirin, wanda Sanata David Umaru ya gabatar, da kuma wadda Sanata Shehu Sani ya gabatar, sun yi kama da kudurai na dokar kare hakkin dan adam, da na tabbatar da zaman lafiya a kasa.

Ministan shari'ar, ya cire wadannan kudure-kudure ne a lokacin da yake bin kadin batun a gaban kwamitin shari'a na majalisar.

Gwamnati ta hambare shirin majalisar dattijai kan kirkirar wasu sabbin hukumomi

Gwamnati ta hambare shirin majalisar dattijai kan kirkirar wasu sabbin hukumomi

A karshe dai, kwamitin ya amince da sauran kudure kudure da suka shafi sauke zababben gwamna idan jiharsa tana cikin halin ko ta kwana kan batun zaman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

A bayanin Ministan shari'ar, "bama son a dinga samun kudurai da hukumomi masu kama da juna, amma sauran kudurai zasu sami shiga."

Shugaban majalisar dattijai Sen. Bukola Saraki, ya yaba da kudurin da aka sami zartarwa, ya kuma sha alwashin goyon baya ga ayyukan da gwamnati ta sanya a gaba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel