Ba zan taba neman gafara wajen Saraki da yan koren sa ba – Ndume

Ba zan taba neman gafara wajen Saraki da yan koren sa ba – Ndume

Sanata Ali Ndume, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa ya bayyana cewa ba zai taba neman gafarar majalisar dattawa dangane da dakatar da shi da aka yi na tsawon watanni 6 don ta maida shi bakin aiki.

A wata zantawa da ya yi da manema labarai a Abuja, Ndume ya ce shi a sanin sa bai aikata laifin da ya kai ga dakatarwar da aka yi ma shi ba, don haka bai ga dalilin da zai sa ya nemi gafarar majalisar dattawa a kan lamarin ba.

Ba zan taba neman gafara wajen Saraki da yan koren sa ba – Ndume

Ba zan taba neman gafara wajen Saraki da yan koren sa ba – Ndume

Sanatan ya kara da cewa, komai nisan dare gari zai waye, kuma dakatarwar da aka yi ma shi ba za ta hana shi ci-gaba da taimaka wa mazabar sa ba.

NAIJ.com ta samu labarin cewa wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, a makon da ya gabata, majalisar dattawa ta bukaci Ali Ndume ya nemi gafarar ta, ta yadda za a samu hujjar maida shi bakin aiki.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel