Korar Inyamurai: Yan sanda su zo su kama mu idan sun isa - Matasan Arewa

Korar Inyamurai: Yan sanda su zo su kama mu idan sun isa - Matasan Arewa

Kwanaki hudu bayan da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta shelanta farautar shugabannin gamayyar kungiyoyin matasan Arewa da suka fitar da wata sanarwa mai kunshe da wa’adin watanni uku na ‘yan kabilar Ibo su bar yankin Arewa, su ma matasan sun shelanta wani batu da za ka iya kira da martani ga ‘yan sandan.

An dai ga shugabannin wancan gamayya ta matasan Arewa har zuwa yau na kai komo a dakin taro na Arewa House inda suka ci gaba da gudanar da taruka.

NAIJ.com ta samu labarin cewa wata majiya ta ‘yan sanda ta bayyana cewa matasan sun ci gaba da gudanar da taruka a Arewa House tare kuma da kalubalantar jami’an tsaro da su kama su in sun isa.

Tun a ranar Larabar da ta gaba ne dai gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufa’i ya bayar da umarnin da a kama wadannan matasa da ya kira marasa kishin kasa.

Korar Inyamurai: Yan sanda su zo su kama mu idan sun isa - Matasan Arewa

Korar Inyamurai: Yan sanda su zo su kama mu idan sun isa - Matasan Arewa

‘Yan sanda sun bayyana cewa suna kokarin aiwatar da wancan umarni ne kwatsam kuma a ranar Juma’ar da ta gabata sai kungiyar dattijan Arewa suka fitar da wata sanarwa ta goyon baya ga matasan kan ‘yan kabilar Ibo su bar yankin Arewa.

Wata majiya daga jaridar Vanguard a daren jiya ta nuna cewa goyon bayan dattijan na Arewa garkuwa ce ga matasan.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel