Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

- A duk lokacin zabe, ana samun kiki-kaka kan 'yancin hukumar zabe a Najeriya

- Shugaban kasa ya ki yarda da hanin cewa fada ta nada shugaban zabe

- Kudin INEC a CBN ake ajje shi

A laccar da Farfesa Attahiru Jega ya bayar a Kano, a Mambayya majalisa, mai taken 'Zabe da Adalci', ya yi kira da a aiwaar da duk kudure-kudure da kwamitin Justice Uwais ya gabatar wa fadar shugaban kasa, kan batun damar nada shugaban hukumar zabe.

A kudurin dai, kamata yayi hukumar zabe ta zama mai cin gashin kanta ta ko wanne fanni, don tabbatar da adalci, da ingattacen kuma karbabben zabe.

KU KARANTA KUMA: An tsaga da rabo: Yadda Sanata Dino Melaye ya sha da kyar

A yanzu dai ana nadin shugaban hukumar ne daga fadar shugaban kasa, wanda hakan ke sa ana iya ganin kamar wasu zasu iya amfani da damar domin dora wanda zai yi musu aiki.

Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

Farfesan ya buga misali da kasar Ghana, inda ya ce: "ko a can ma, duk da zabe na kyau, shugaban kasa ne ke nadin, sai dai idan aka nada baya sauka sai ya kai sahekarun ritaya ta ma'aikaci.

"Amma an sami ci gaba, inda a yanzu haka, kudaden hukumar suna zaune ne a babban bankin Najeriya na CBN, kuma muddin shugaban kasa ya rattaba hannu ya saki kudin, to hukumar ce kadai mai yadda zata yi da kudin ta, ba tare da tsangwama ba."

Ana dai shirin fuskantar zabe a cikin shekara mai zuwa, bayan da aka sami rabin wa'adin shekarun gwamnati mai ci a yanzu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel