An gudanar da bukin ranar yaki da bautar da kanana yara ta duniya

An gudanar da bukin ranar yaki da bautar da kanana yara ta duniya

- An gudanar da bukin ranar yaki da bautar da kanana yara ta duniya

- Kungiyar kwadago ta duniya ta ce kimanin yara miliyan 168 yan shekaru 5 zuwa 14 da suke aikin kwadago a kasashen Afrika ta yamma

- Yara miliyan 15 a Najeriya kawai suke aikin kwadago a sassan daban-daban a kasar

Kungiyar kwadago ta duniya ta fidda rahoton dake bayani cewa a duniya baki daya akwai kimanin yara miliyan 168 yan shekaru 5 zuwa 14 da suke aikin kwadago wanda daga ciki yara miliyan 15 a Najeriya suke wanda hakan na nuni da cewar kasar itace ke da mafiya yawa a kasashen Afrika ta yamma.

Wasu yaran sun bayyana cewar idan mutum na sana’a yafi, saboda a sana’ar da suke yi suna samun naira 300 ko 200 ko kuma kasa da hakan. Wani yaron yace mahaifinsa ne ya kaishi koyon dinki kuma a wannan aiki yana samun abin kashewa.

KU KARANTA: June 12: Shin meye muhimmancin wannan rana ga Kabilar Yarabawa? Dama Najeriya?

Shugaban shiyar Arewa maso gabacin Najeriya ta kungiyar kare hakkin mata da yara ta Women’s Situation Room tace yara dayawa da suka rasa iyayensu ko kuma daya daya a cikin iyayen suna zaune kara zube, sune ake turawa suje su kawo abin da za a ci kuma hakan ne ke kai ga fadawan kananan yara a cikin ayyukan kwadago wani lokacin ma har a ci zarafinsu.

An gudanar da bukin ranar yaki da bautar da kanana yara ta duniya

Kimanin yara miliyan 168 yan shekaru 5 zuwa 14 da suke aikin kwadago a kasashen Afrika ta yamma

Shugaban kungiyar Women’s Situation Room tace gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu suna alhakin samarwa yaran gidajen marayu inda za a kai irin wadannan yara ana kula da su ba sai sun je waje neman kudi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A cikin wannan bidiyon 'yan albinu sun bayyana matsalolin da suke fuskanta a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel