An tsaga da rabo: Yadda Sanata Dino Melaye ya sha da kyar

An tsaga da rabo: Yadda Sanata Dino Melaye ya sha da kyar

– Saura kiris wasu ‘yan bindiga su hallaka Sanata Dino Melaye

– Sai dai fa har yanzu Sanatan ya gudu ne bai tsira ba

– Melaye yana cikin wana hali na ha’ula’i a yanzu

Sanata Dino Melaye ya tsallake rijiya da baya. Har yanzu dai kuma akwai wata rijiyar a gaban sa

Sanatan yace wasu sun nemi su kashe shi.

Sanata Dino Melaye

Saura kiris a hallaka Sanata Dino Melaya a mota

Kun ji cewa Sanata Dino Melaya ya ga uwar bari inda wasu su ka kai masa hari yayin da yake wani taro a wata makaranta da ke Garin Lokoja. Wasu ne dai su kai hari da bindiga da wasu makamai a wurin.

KU KARANTA: Wasu Inyamurai sun ce babu ruwan su da ballewa

Wannan abu dai ya kai har aka rasa rai guda inda shi kuma Sanatan ya sha da kyar. Mun ga wani sako inda Sanatan yake kokarin ya nuna cewa ba don harsashi bai iya huda motar sa ba da yanzu labari ya canza.

Haka dai kwanaki aka yi kokarin kashe Sanatan wanda Jaridar Sahara Reporters tace Sanatan ne kurum yake wasan kura da hankalin Jama’a. Har yanzu dai Dino Melaye na cikin tsaka mai wuya don kuwa Mutanen Yankin san a shirin yi masa kiranye.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Su wa su ka fi karya tsakanin maza da mata?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel