Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya nada yan Najeriya 10 zuwa hukumar CCB

Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya nada yan Najeriya 10 zuwa hukumar CCB

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya nada ‘yan Najeriya 10 a matsayin mambobin hukumar yaki da rashawa wato hukumar Code of Conduct Bureau (CCB).

Nadin ya zo ne cikin kasa da sa’o’I 24 bayan Farfesa Osinbajo ya sanya hannu a kasafin kudin shekarar 2017 wanda aka jinginar tsawon watanni da dama.

Mista Mohammed Nakorji, mataimakin daraktan dake kula da harkokin labarai a ofishain Sakataren gwamnatin tarayya , ya lissafo sabbabin mutanen da aka nada.

1. Dr Muhammad Isah daga Jigawa a matsayin shugaba

KU KARANTA KUMA: Yayin da ake maganar raba kasa: Osinbajo ya kama hanyar kasar Inyamurai

2. Murtala Kankia daga Katsina a matsayin mamba

3. Emmanuel E Attah daga Rivers a matsayin mamba

4. Danjuma Sado daga Edo a matsayin mamba

5. Ubolo I Okpanachi daga Kogi a matsayin mamba

6. Ken Madaki Alkali daga Nasarawa a matsayin mamba

7. Farfesa SF Ogundare daga jihar Oyo a matsayin mamba

8. Hon Ganiyu Hamzat daga Ogun a matsayin mamba

9. Sa’ad A Abubakar daga Gombe a matsayin mamba

10. Dr Vincent Nwanli daga Ebonyi a matsayin mamba

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali yayinda gadar Jebba ya rushe

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ratabba hannu kan kasafin kudin Najeriya na bana.

Mukaddashin Shugaban kasar ya sa hannun a Ofishin shugaban kasa inda Najeriya za ta kashe sama da Tiriliyan 7 a bana.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com TV da Yemi Osinbajo ke magana a kan yakin Biyafara.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel