Biafra: Bamu goyon bayan Nnamdi Kanu, garambawul kawai muke so – Ohanaeze Ndigbo

Biafra: Bamu goyon bayan Nnamdi Kanu, garambawul kawai muke so – Ohanaeze Ndigbo

Kungiyar gamayyar yan kabilar Igbo, – Ohanaeze Ndigbo - ta nisanta kanta da yakin neman yancin Biafra da Nnamdi Kanu da kungiyarsa, Indigenous People of Biafra (IPOB).

Ohanaeze Ndigbo ta nanata cewa garambawul kawai ne maifita ga rikicn siyasa da tattalin arzikin Najeriya, ba ballewa ba.

Mataimakin kakakin Ohanaeze Ndigbo, Chuks Ibegbu, ya bayyana wannan ne a wata hira da manema labarai ranan Litinin.

Biafra: Bamu goyon bayan Nnamdi Kanu, garambawul kawai muke so – Ohanaeze Ndigbo

Biafra: Bamu goyon bayan Nnamdi Kanu, garambawul kawai muke so – Ohanaeze Ndigbo

Yace: “Kasa Najeriyan da zata baiwa kowani sashe hakkin ta. Misali, kasa mai jihohi 36, yankin kudu maso yamma na kananan hukumomi 95 amma jihar Kano kadai na da kananan hukumomi 44.

KU KARANTA: Sanata Kanti Bello yayi nadaman zaban Buhari

“Kwanaki, munga aikin da aka dauka a hukumar DSS inda jihar Katsina kadai ta samu wuri 51. Muna bukatan EFCC tayi bincike kan daukan aikin DSS. jihar Abia wuri 6 ta samu, Enugu 6 ta samu, amma jihar shugaban kasa ta samu 51.

“Ba wai muna cewa a raba Najeriya bane, amma abinda wadannan matasan ke fada ya kamata a duba shi.”

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel