Kasafin kudi: Wurare 5 da Gwamnatin Buhari za ta ba karfi

Kasafin kudi: Wurare 5 da Gwamnatin Buhari za ta ba karfi

– Farfesa Osinbajo yace Gwamnatinan za ta fi maida hankali ne kan abubuwa 5

– Daga ciki dai akwai harkar noma domin samun isasshen abinci

– Za kuma a gyara hanyoyin kasar daga yanzu zuwa 2020

A cikin inda wannan Gwamnati ta ba karfi akwai harkar wuta

Gwamnatin Buhari kuma za ta taimakawa kananan ‘yan kasuwa

Osinbajo ya bayyana yadda Najeriya za ta kashe sama da Tiriliyan 7 a shekarar nan

Kasafin kudi: Wurare 5 da Gwamnatin Buhari za ta ba karfi

Gwamnatin Buhari za ta dage wajen aikin noma

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Gwamnatin su ta fi ba abubuwa 5 karfi wanda dai ga su kamar haka:

1. Harkar noma

Tun can wannan Gwamnati ta dage wajen harkar noma domin samun isasshen abinci a fadin kasar.

2. Ba da damar kasuwanci

Gwamnatin APC za ta kawo sauki wajen harkar gudanar da sha’anin kasuwanci a cikin Najeriya ta haka ne ‘yan kasuwa da masu jari za su ji dadin ba-ja-koli.

KU KARANTA: An fito domin a gaida Osinbajo a filin jirgi

Kasafin kudi: Wurare 5 da Gwamnatin Buhari za ta ba karfi

Buhari zai ba noma da kasuwanci muhimmanci

3. Lantarki

A cikin inda wannan Gwamnati za ta ba karfi daga yanzu zuwa shekarar 2020 akwai harkar wuta da kuma harkar man kasar.

4. Hanyoyi

Osinbajo yace za kuma a gyara hanyoyin kasar daga bana zuwa 2020 domin daukar kayan amfani da mutane.

5. ‘Yan kasuwa

Gwamnatin APC za ta taimakawa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa wanda hakan zai taimaki tattalin kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tattunawa da Nnmadi Kanu da kuma tawagar sa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel