Kasafin kudi: Ko ka san bashin Tiriliyan nawa Najeriya ke shirin karbowa

Kasafin kudi: Ko ka san bashin Tiriliyan nawa Najeriya ke shirin karbowa

– Osinbajo yace Gwamnatin Tarayya za ta ci bashin sama da Tiriliyan 2

– Najeriya za ta kashe sama da Tiriliyan 7 a shekarar nan

– Farfesa Osinbajo yace daga ciki za a ci bashi ne na Tiriliyan 2

Jiya Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya sa-hannu kan kundin kasafin kudin bana

Farfesan yace Najeriya na shirin kashe Naira Tiriliyan 7 da Biliyan 400 shekarar bana

Sai dai daga ciki sai an nemo bashin Tiriliyan 2 da Biliyan 300 da Miliyan 60.

Kasafin kudi: Ko ka san bashin Tiriliyan nawa Najeriya ke shirin karbowa

Lokacin da Osinbajo zai rattaba hannu kan kundin kasafin kudi

Mukaddashin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya rattaba hannu kan kasafin kudin wannan shekara inda Najeriya ke shirin kashe Tiriliyan 7.44. Daga ciki dai dole kasar ta ci bashi domin cike gibin da za a samu.

KU KARANTA: An rattaba hannu kan kasafin bana

Kasafin kudi: Ko ka san bashin Tiriliyan nawa Najeriya ke shirin karbowa

Najeriya za ta karbi bashin Tiriliyan 2 a bana

Ana sa rai Najeriya za ta samu kudin shiga har Tiriliyan 5.08 wanda zai sa dole a ci bashin kusan Tiriliyan 2.36 domin cike abin da ake bukata na sama da Tiriliyan 7. Najeriya dai za ta kashe sama da Miliyan 500 wajen gyaran hanyoyi.

Kuna da labarin cewa Farfesa Osinbajo yace za ayi amfani da kudin da aka karbe daga hannun barayi wajen yi wa Najeriya ayyukan a zo-a gani.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sababbin Jam'iyyu za su share mana hawaye kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel