Shugaba Buhari na taya wasu 'yan Najeriya murnar cin zabe a Burtaniya

Shugaba Buhari na taya wasu 'yan Najeriya murnar cin zabe a Burtaniya

- An sami mutum 7 'yan asalin Najeriya sun ci zabukan majalisa ta kasar Ingila

- Wadanda suka ci zaben sun yi takara ne a jam'iyyun kasar kuma an zabe su ba tsangwama

- Sanarwa daga fadar shugaba Buhari ta taya zababbun murna

A sanarwar da fadar shugaban kasa ke fitarwa da sunan shugaba Buhari, sanarwar baya-bayan nan ta fito inda da yawun shugaban ake taya 'yan Najeriya da suka sami damar cin zabuka da aka yi a kasar Burtaniya, wadanda aka zabo su babu tsangwama.

Sanarwar ta kira sunayen wadanda suka ci zaben kamar haka, Chi Onwurah (Newcastle), Kate Osamor (Edmonton), Kemi Badenock (Saffron Walden) and Bim Afolani (Hitchin & Harpenden). Sai kuma Chuka Umunna (Streatham), Fiona Onasanya (Peterborough) and Helen Grant (Maidstone & The Weald).

Shugaba Buhari na taya wasu 'yan Najeriya murnar cin zabe a Ingila

Shugaba Buhari na taya wasu 'yan Najeriya murnar cin zabe a Ingila

Sanarwar wadda ta fito daga bakin Abike Dabiri Erewa, mai baiwa shugaba Buhari shawara kan 'yan Najeriya mazauna kasashen waje, ta yaba da kwazon su da kuma taya su fatan iya tafiyar da aikin nasu bisa adalci da kyautayi, ta kuma kara da cewa, nasarar tasu na kara fito da hazakar 'yan Najeriya a duk inda suka shiga a fadin duniya.

An dai sami karuwar hazikan mutanen Najeriya dake sassa daban daban na duniya, inda a lokacin da tsana ke kara yaduwa a cikin jama'ar kabilun kasar, su kuma na kasar wajen suna kara zama hazikan baki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel