Boko Haram: An cafke mayakan Boko Haram a jihar Edo

Boko Haram: An cafke mayakan Boko Haram a jihar Edo

- An kama wasu 'yan Boko Haram da suka yi shigar burtu don kai hare-hare a jihar Edo

- An gano su a maboyarsu a daji, inda sukayi shigar fulani makiyaya

- Sarkin Auchi ya shawarci mata da su dena zuwa gona saboda yawan hare-hare a kansu

A jihar Edo ta Najeriya, jiha mai arzikin man fetur, an kama wasu mayakan Boko Haram da suka sulala cikin kasar don tada zaune tsaye, an kama su a cikin dazuka inda suka makale kamar 'yan fulani masu kiwo.

An sami karuwar hare-hare na fulani makiyaya a kasashen kudancin kasar nan, har ta kai ba'a iya zuwa gonaki saboda fyade da hare-haren masu shigar fulani a kasashen kudu, wanda hakan ke zafafa kalamai tsakanin kabilun kasar nan.

Boko Haram: An cafke mayakan Boko Haram a jihar Edo

Boko Haram: An cafke mayakan Boko Haram a jihar Edo

Mai martaba, Alhaji Aliru H. Momoh, Otaru na masarautar Auchi, jihar Edo shine ya bada sanarwar inda ya bada yawan maharan har su 24. Ya kuma ce an tura su babban birnin jihar Benin domin tuhuma a kotu.

Mai martaban, ya kara da cewa, yanzu yana baiwa mata manoma jari don su daina zuwa gona, zuwa lokacin da za'a shawo kan matsalar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel