Allah yayi: Osinbajo ya sa hannu kan kasafin kudin 2017

Allah yayi: Osinbajo ya sa hannu kan kasafin kudin 2017

– Mukaddashin Shugaban Kasa Osinbajo ya sa hannu kan kasafin kudin bana

– Osinbajo yace wannan zai taimakawa tattalin arzikin Najeriya

– Shugabannin Majalisa sun halarci taron sa hannun

An ratabba hannu kan kasafin kudin Najeriya na bana

Mukaddashin Shugaban kasa ya sa hannun a Ofishin shugaban kasa

Najeriya za ta kashe sama da Tiriliyan 7 a bana

Farfesa Osinbajo

Farfesa Osinbajo ya sa hannu kan kasafin kudin 2017

Shugabannin Majalisa Sanata Bukola Saraki da Honarabul Yakubu Dogara sun halarci taron sa-hannun kundin kasafin kudin bana a fadar shugaban kasa. An dai dauki dogon lokaci ba a rattaba hannu kan kasafin ba.

KU KARANTA: Za a sa hannu kan kasafin kudin bana

Allah yayi: Osinbajo ya sa hannu kan kasafin kudin 2017

Shugabannin Majalisa wajen taron dazu

Farfesa Yemi Osinbajo ya sa hannu daidai karfe 4: 42 na yammacin yau tare da wasu Ministocin kasar da masu ba shugaban kasa shawara kan harkokin Majalisa. Osinbajo yace wannan kasafin na Gwamnatin Buhari zai babbako da tattalin arziki.

Dazu kun ji Farfesa Osinbajo yace ba zaman jiran Shugaban kasa ya sa aka dauki dogon lokaci kundin kasafin kasar na tangal-tangal ba. Har yanzu Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai dawo daga Kasar Ingila inda yake jinya ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sababbin Jam'iyyu za su taimaka wajen gyara Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel