'Aiki da Buhari yafi komai sauki, saboda gaskiyarsa' - Inji hadimarsa

'Aiki da Buhari yafi komai sauki, saboda gaskiyarsa' - Inji hadimarsa

- 'Gaskiyar Buhari ta sa ba'a wahala a kan aiki da shi'

- 'A wasu kasashen saboda karyar shuwagabanni, aikin ma'aikatansu yana da bakar wahala'

- Lauretta Onochie ita ce mai taya shugaba Buhari da harkar hanyoyin sada zumunta

A hirarta da jaridar Punch, mai taimakawa shugaba Buhari da harkar sadarwar zamani, Lauretta Onochie, tace aikin ta da Buhari yana da matukar sauki.

Ta kwatanta wadansu shuwagabannin da cewa saboda kwabarsu da karyarsu, sai ya zamanto ma'aikatansu sai sun ta kwabo karya don rufe wa shugaban nasu asiri.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari na taya wasu 'yan Najeriya murnar cin zabe a Burtaniya

'Aiki da Buhari yafi komai sauki, saboda gaskiyarsa' inji hadimarsa

'Aiki da Buhari yafi komai sauki, saboda gaskiyarsa' inji hadimarsa

Tace tayi takaicin yadda wasu ke fatan shugaba Buhari ya mutu, duk da cewa yafi kowa gaskiya, sannan kuma tace shugaba Buhari yayi babban katabus a shekaru biyu da yake kan mulki.

"Duk wanda yace shugaba Buhari bai iyaba, to bayyi adalci ba, ai canji ba dare daya ake ganinsa ba, a'a, kullum ana tafiyar da canjin ne sai ya samu a hankali."

Ta ce masu yi wa shugaban mugun fata, sun kasa shake shi ne, shi yasa suke masa fatan mutuwa, saboda ya mutu su gaje dukiyar da ya kwato daga hannunsu, inda tace sai dai suje su yi tsafi da asiri, kuma Allah ya fi su.

A baya dai an sami sa'in sa tsakanin Miss Lauretta da Fani Kayode kan batun suka ko yabon Buharin, ta kuma caccaki Malama Aisha Yesufu ta BBOG kan batun 'yan matan Chibok, da ma batun wai yayi murabus ya je jinya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel