Ramadan: A kauce wa kallon talabijin yayin yi addu’a – Inji wani babban malami

Ramadan: A kauce wa kallon talabijin yayin yi addu’a – Inji wani babban malami

- Wani babban malami ya shawarci al’ummar musulmai cewa su kauce wa kallon talabijin yayin yi addu’a

- Malamin ya bukaci musulmai su yi amfani da damar watan Ramadan domin yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a

- Seriki ya bukaci masu hannu da shuni musamman musulmai da su taimaka wa marasa galihu

Wani babban malamin addinin musulunci, Alhaji Aminulahi Seriki, a ranar Lahadi, 11 ga watan Yuni ya yi kira ga 'yan Najeriya musamman musulmai cewa su yi amfani da damar watan Ramadan domin a yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a game da rashin lafiyarsa.

Seriki wanda shine mataimakin babban Iimamin masallacin Ansarul-deen da ke unguwar Fadeyi a Legas ya yi wannan kiran a wani lacca na shekara da shekara a watan Ramadan, mai suna '' Tasirin yi addu’a.”

NAIJ.com ta ruwaito cewa Alhaji Moshood Salvador ya shirya wannan lacca, kuma shine shugaban wani bangaren jam’iyyar PDP a jihar Legas.

Ramadan: A kauce wa kallon talabijin yayin yi addu’a – Inji wani babban malami

Shugaba Muhammadu Buhari da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo

Malamin, wanda ya bayyana cewa Allah ya umarce al’umma da su yiwa shugabanninsu addua, ya bukaci Musulmai su kauce wa kallon talabijin yayin da suke addu'a don addu’an su ya samu karba.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa wasu yan Najeriya ke son shugaba Buhari ya mutu – Fadar shugaban kasa

Seriki ya ce: “ Ya kamata mu mayar da hankalin mu gaba daya ga Allah a duk lokacin da mu ke addu'a ga Allah.”

"Bai kamata ana duba talabijin ko kalle-kallen abubuwa dake faruwa a kusa da kai yayin yin addu'a. Irin wannan abubuwa ne ke sanadin rashin karba addu'a cikin lokaci.” Inji malamin

Seriki na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na bukatar addu'o'in 'yan Najeriya don maido da kiwon lafiyarsa da kuma samu shiryarwar Allah a mulkinsa.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai su yi addu'a domin samu zaman lafiya da hadin kai na kasar.

Seriki ya bukaci masu hannu da shuni musamman musulmai da su taimaka wa marasa galihu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya kamata shugaba Buhari ya mika wa mataimakin shugaban kasar Osinbajo mulki kan kiwon al'amurran da suka shafi lafiyasa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel