2019: 'Buhari ya gaza, dole mu kawar dashi' - Kanti Bello

2019: 'Buhari ya gaza, dole mu kawar dashi' - Kanti Bello

- Sanata Kanti Bello ya ballo ruwa

- Ya ce yayi da-na-sanin tsoma Buhari a harkar siyasa

- 'Zan yi yadda zanyi don korar Buhari a 2019'

A shirin zaben da ke tafe, na 2019, Sanata Kanti Bello wanda ya fito daga mazaba daya da shugaba Buhari, ya ce shugaban ya gaza a mulkinsa, kuma ma ba yadda za'ayi ya bari a sake zabarsa a matsayin shugaban kasa, inda yace zayyi duk yadda zaiyi yayi kanfe na kar a zabi shugaban.

Jam'iyya daya dai suka fito, da shugaba Buhari da Sanata Kanti Bello, wanda ya taba yin Sanata a Katsina ta arewa, ya kuma yi ikirarin shi ne ma ya tsunduma shugaban a harkar siyasa tun bayan dawowar dimokuradiyya a 2002.

KU KARANTA KUMA: LABARI DA DUMI-DUMI: Manjo Al’Mustafa na ganawa da shugaban kungiyar fafutukar Biyafara

2019: 'Buhari ya gaza, dole mu kawar dashi' Kanti Bello

2019: 'Buhari ya gaza, dole mu kawar dashi' Kanti Bello

Ya kuma ce 'yan bambadannci ne kawai suka makale shugaba Buharin don haka basu iya fadin gaskiya. Ya kuma ce tuni ma su manyan APC sun fara neman wanda zasu tsayar yayi musu takara a 2019, domin wai yar da shugaba Buhari zasu yi.

"Batun ba wai na yaki da rashawa bane, a'a, sai fa an sami abin sawa a ciki ma za'a fuskanci wani yaki da rashawa, ni da kaina zan hau mumbari in yi kwakwazon kar a sake zabar shugaba Buhari," inji Sanatan.

A badi dai za'ayi zabukan fidda gwani a jam'iyu na kasa baki daya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel