Kungiyar mata sun yi ma shugaba Buhari addu’a

Kungiyar mata sun yi ma shugaba Buhari addu’a

- Kungiyar mata sun shirya taron yi ma shugaba Buhari addu’an samu lafiya tare da sauran yan siyasa

- Sun kuma yi kasar addu'a tare da mika al'amuran kasar a hannun Ubangiji

- Daga karshe sun tallafa wa zawarawa da gajiyyayu

Wani kungiyar mata sun shiya taron yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’an samu lafiya.

Matan sun tattaru ne a hedkwatar karamar hukumar Obowo dake jihae Imo sannan kuma sun mika al’amuran kasar a hannun Allah sannan kuma sukayi ma addu’a kan Allah yak are dukkan shugabannin siyasa a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatinmu ta jama'a ce - inji wani gwamnan arewa

Wadanda suka shirya taron sunyi amfani da daman gurin tallafawa zawarawa da marsa karfi ta hanyar basu kayayyakin abinci da kudade.

A halin da ake ciki, manyan malamai guda dari biyar sun yi addu’a na musamman don samun lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ci gaban kasar.

Gwmnatin jihar Zamfara ne ta shirya taron inda aka tattara manyan malaman daga kananan hukumomi 14 a jihar Zamfara

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon hiran shugaban kungiyar Biyafara Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel