Harin ýan bindiga: Sanata ya tsallake rijiya da baya

Harin ýan bindiga: Sanata ya tsallake rijiya da baya

- Sanata Dino Melaye ya sha da kyar yayin da wasu yan bindiga suka kai masa hari

- An kai masa harin ne a gaban kwalejin kimiyya da fasaha

Sanatan mai wakiltar al’ummar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya sha da kyar yayin da wasu yan bindiga suka kai masa harin ba zata a garin Lokoja, inji rahoton jaridar Tribune.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito harin ya wakana ne a ranar Litinin 12 ga watan Yuni a gab da kwalejin kimiyya da fasaha na jihar Kogi.

KU KARANTA: Jana’izar dan kwallo Tiote: Jama’a sun koka (Hotuna/bidiyo)

Majiyar ta bayyana cewar Sanata Melaye ya tsaya ne a gaban kwalejin domin ya gana da magoya bayansa dangane da rikicin siyasan data dabaibaye jihar Kogi, ana cikin haka ne sai kawai yan bindiga suka fito daga yakin NATCO suna harbin mai kan uwa da wabi.

Harin ýan bindiga: Sanata ya tsallake rijiya da baya

Sanata Melaye

An kwashe kimanin mintuna 30 ana harbe harben, wanda hakan yayi sanadiyyar cushewar ababen hawa a kan titin Lokoja zuwa Abuja.

Shima Sanata Melaye ya tabbatar da harin a wasu bayanai daya fitar a shafinsa na Tuwita, inda yace an raunata mutane biyu da kuma kona motocinsa guda biyu.

Harin ýan bindiga: Sanata ya tsallake rijiya da baya

Melaye

A wani labarin kuma, Sanatan ya mayar da martani game da yunkurin yi masa kiranye da ake yi a mazabarsa, inda ya zargi gwamnan jihar Yahaya Bello a matsayin mutumin daya shirya shirin yi masa kiranyen.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rayuwar mutanen yan kan titi:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel