Korar Kabilar Ibo daga Arewa: 'Baza ku ingiza mu muyi yaki ba' Ibo mazauna kasar Yoruba

Korar Kabilar Ibo daga Arewa: 'Baza ku ingiza mu muyi yaki ba' Ibo mazauna kasar Yoruba

- Sun yaba da matakin gwamna Nasir El-Rufai

- An sami musayar kausasan kalamai tsakanin kabilun Ibo da Hausawa

- Ibo sun gano cewa so ake a raba kan yan Najeriya a kuma ingiza su zuwa yaki

Kabilar Ibo mazauna jihar Oyo, babban birnin kabilar Yarabawa, sun yi tsokaci kan yadda ake kokarin ingiza kabilarsu ga yaki da kabulun Hausawa na arewa, da cewa wai sai kowanne bangare ya koma inda ya fito, inda suka ce lallai wannan manakisa ce a cuce su.

Sun ce ba wata kalma ta batanci, ko tunzurawa da zata kaisu ga shiga yaki da wata kabila a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: 'Aiki da Buhari yafi komai sauki, saboda gaskiyarsa' - Inji hadimarsa

Kalaman na fitowa ne daga OnyeOlu of IbadanLand, Cif Aloy Obi, sarkin Ibo mazauna Ibadan, yace wadanda suke son ingiza ko kuma yakar Ibo su san sashe na 42 na kundin tsarin mulki ya ba kowa dama yaje ya zauna inda yake so cikin fadin Najeriya.

Ya kuma yaba da matakin da gwamnan jihar Kaduna ya dauka na bada umarnin cafke masu son tada zaune tsaye a jihar Kaduna, ya kuma soki hukumomi ciki harda yan sanda kan kin bin diddigi da daukar matakai musamman ganin jama'un kabilun wasu yankuna tuni sun fara komawa gida.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel