Masu tayar da kayar baya sun saki Saif dan Mu'ammar Gaddafi

Masu tayar da kayar baya sun saki Saif dan Mu'ammar Gaddafi

- An saki Saif al-Islam, ɗa na biyu ga marigayi shugaban Libya Kanar Muammar Gaddafi daga gidan kurkuku bayan an yi masa afuwa.

- Saif al-Islam, wanda a baya aka yi zaton shi zai gaji mahaifinsa, ya shafe kusan shekara shida a hannun masu tayar da kayar baya a garin Zintan.

Kungiyar masu tayar da kayar bayan ce ta sanar ranar Asabar cewa ta sake shi.

A 2015 ne wata kotun da ke birnin Tripoli ta yanke masa hukuncin kisa amma kungiyar ta ki amincewa ta mika shi.

A baya an bayar da rahoton karya cewa an sake shi.

Masu tayar da kayar baya sun saki Saif dan Mu'ammar Gaddafi

Masu tayar da kayar baya sun saki Saif dan Mu'ammar Gaddafi

NAIJ.com ta samu labarin cewa kotun hukunta masu aikta manyan laifuka ta duniya, ICC tana nemansa ruwa-a-jallo domin yi masa shari'a kan zargin aikata laifuka take hakkin dan adam lokacin da mahaifinsa ya yi yunkurin murkushe 'yan adawa.

An kama Saif al-Islam, mai shekara 44, a watan Nuwamba na 2011 bayan ya kwashe wata uku yana buya sakamakon tumbuke gwamnatin mahaifinsa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel