Korar Inyamurai: Dan majalisar tarayya daga Kano ya goyi bayan matasan Arewa

Korar Inyamurai: Dan majalisar tarayya daga Kano ya goyi bayan matasan Arewa

Wani dan majalisar tarayya ta wakillai mai wakiltar jihar Kano ya bayyana goyon bayan sa ga matasan arewa da suka umurci inyamurai su bar yankin Arewa kafin wata uku da ke tafe.

NAIJ.com kuma ta samu cewa dan majalisar wakilan mai suna Aminu Suleiman wanda kuma shine shugaban kwamitin dake kula da harkokin manyan makarantu yace mutanen kasar na yankin inyamurai ba za'a bar su su addabi kasar baki daya ba da rashin da'ar da suke nunawa.

"Na karanta sanarwar da matasan na arewa suka fitar kuma duk da dai ban yadda da duka abun da suka ce ba amma tabbas suna da gaskiya a wani bangaren."

A wani labarin kuma, Rahotanni sun bayyana cewa, Manjo Al’mustapha wanda shine tsohon babban jami’in mai tsaron lafiyar marigayi shugaba Janar Sani Abacha zai yi wata muhimmiyar ganawa da kungiyoyin matasan arewa don ganin an zauna lafiya tsakanin al’ummar Arewa da‘yan kabilar Igbo.

Korar Inyamurai: Dan majalisar tarayya daga Kano ya goyi bayan matasan Arewa

Korar Inyamurai: Dan majalisar tarayya daga Kano ya goyi bayan matasan Arewa

A jihar Kaduna ne za a gudanar da wannan taro wanda za ta kunshi fahimtar juna tsakanin yankunan biyu bisa dagewa da masu rajin kafa kasar Biafra keyi da kuma wa’adin sallamar ‘yan kabilar Igbo daga Arewa da wasu kungiyoyi suka bayar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel