Fasto ya musulunta bayan sauraron Tafsiri a jihar Ribas (Hoto)

Fasto ya musulunta bayan sauraron Tafsiri a jihar Ribas (Hoto)

- Wani Fasto a garin Fatakwal ya musulunta bayan sauraron Tafsiri a jihar Ribas

- Tuni dai wannan bawan Allah dayaga haske yayi wanka

Wani rahoto daga jaridar Rariya ya bayyana cewar wani Fasto a garin Fatakwal ya musulunta bayan sauraron Tafsiri a jihar Ribas.

Majiyar NAIJ.com ta shaida cewar wannan Fasto ya musulunta ne a masallacin dake sansanin ajiye manyan motoci Tireloli dake unguwar Eleme an jihar Ribas.

KU KARANTA: Sojoji sun gudanar da aikin gayya a jihar Legas (Hotuna)

Tuni dai wannan bawan Allah dayaga haske yayi wanka kuma aka fara koyar da shi addini.

Fasto ya musulunta bayan sauraron Tafsiri a jihar Ribas (Hoto)

Faston daya musulunta

Ko a kwanakin baya cikin wannan Azumin Ramada da muke ciki, NAIJ.com ta ruwaito wani matashin kirista ne daya musulunta a jihar Sakkwato bayan ya halarci taron wa’azin Tafsiri a wani Masallaci dake Unguwar Koko cikin birnin Sakkwato.

Limamin Masallacin Ali Bn Abi Talib, Malam Bashar Ahmad Sani ne ya baiwa wannan matashi kalmar shahada, inda nan take ya musulunta kuma ya sauya suna.

Dama dai ana yawan samun jama’a wadanda ba Musulmai ba suna karbar addinin Musulunci, musamman a watan Azumi yayin da ake gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani mai girma, don ko a Azumin bara an samu sabbin Musulmai da dama maza da mata a masallatai daban daban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana yi ma Dino Melaye shirin kiranye:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel