'Buhari azzalimi ne da ya fake da cewa wai yana yakar barayin gwamnati'

'Buhari azzalimi ne da ya fake da cewa wai yana yakar barayin gwamnati'

- Ya kasa bin dokar kotu kan Col. Sambo Dasuki'

- Afenifere kungiya ce ta Yarabawa zalla

- 'Kasar nan zata balle'

Shugaban kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, Cif Ayo Adebanjo, ya ce shugaba Buhari azzalumi ne da ya fake da cewa wai shi gwarzon mai yaki da cin hanci ne, domin a cewar sa, ya kasa bin umarnin kotu kan sakin Col. Sambo Dasuki.

Ya kara da cewa shugaba Buharin ya kasa magana kan mahara fulani makiyaya da ke kai hare-hare.

A cewarsa, kasar Najeriya baza ta dore ba, balle wa zatayi saboda sakaci da bangaranci irin na Buhari.

'Buhari zalimu ne da ya fake da cewa wai yana yakar barayin gwamnati'

'Buhari zalimu ne da ya fake da cewa wai yana yakar barayin gwamnati'

"Na hanga a mahanga ta cewa kasar nan zata balle', yace. 'ba ma sai ka jira wata shaida ba.

"In ba zalunci ba, mahara na makiyaya suna ta kai hare-hare, amma tsit kake ji, ba wanda aka taba kamawa, wataran wadanda ake zalunta zasu tashi tsaye ai." inji shi.

Kungiyar Afenifere dai ta Yarabawa zalla ta mara wa shugaba Buhari baya a lokacin da yake neman mulki a jam'iyyar APC.

Ga dukkan alamu kuma akwai rina a kaba muddin jam'iyyar ta sake tsayar dashi takara, domin karbuwa a yankin na Yarabawa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel