Duk wanda ba'a sa ma na'urar mita ba to kada ya sake biyan kudin wutar lantarki - Gwamnatin tarayya

Duk wanda ba'a sa ma na'urar mita ba to kada ya sake biyan kudin wutar lantarki - Gwamnatin tarayya

Hukumar kaiyade harkokin wutar lantarki ta kasa,NERC, ta umarci masu amfani da wutar lantarki da ba’a samarwa da mita ba daga ranar 1 ga watan Maris da su daina biyan kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki kudi.Karkashin tsarin nan na kiyasin adadin wutar da sukayi amfani da ita.

Hukumar ta kuma umarci kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki da kada sun yanke wutar duk wanda bai biya kudi ba, ta kuma shawarci jama’a da sukai rahoton yanke musu wutar lantarki ga hukumar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa NERC, ta bada wannan umarnin ne a wata sanarwa da ta saka a shafinta na yanar gizo, inda tace hakan wani bangare ne na hukunta kamfanonin da suka saba yarjejeniyar samar na’urar mitar ga abokanan huldarsu kafin wa’adin 1 ga watan Maris.

Duk wanda ba'a sa ma na'urar mita ba to kada ya sake biyan kudin wutar lantarki - Gwamnatin tarayya

Duk wanda ba'a sa ma na'urar mita ba to kada ya sake biyan kudin wutar lantarki - Gwamnatin tarayya

Karkashin kudirinta na kare hakin masu amfani da hasken wutar lantarki, a watan Yunin shekarar 2016, bayan tattunawa da kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki hukumar ta umarci kamfanonin da su kammala samarwa da abokanan huldarsu mitoci kafin ranar 30 ga watan Nuwambar shekarar 2016.

A cewar hukumar ta karawa kamfanonin wani wa’adin wata uku wanda zai kare ranar 1 ga watan Maris.domin basu damar aiwatar da umarnin.

Hukumar tace ta dau wannan mataki ne, biyo bayan cikar wa’adin da ta bawa kamfanonin da kuma cikar karin wa’adin da ta sake yi musu a ranar 1 ga watan Maris. Sanarwar tace:

” An umarci kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki da su samar da mitoci ga dukkanin abokan huldarsu da basu da ita kafin 30 ga watan Nuwamabar, 2016.

“Hukumar ta karbi korafi daga kamfanonin kafin wa’adin ya kare,an kara wa’adin zuwa ranar 1 ga watan Maris bayan duba korafin kamfanonin da hukumar tayi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel