Boko Haram ta fitar da sharudɗan yin sulhu da gwamnati

Boko Haram ta fitar da sharudɗan yin sulhu da gwamnati

- Madugun Boko Haram ya gindaya sharudɗan zaman lafiya

- Shugaban kungiyar yan ta’adda na Boko Haram, Abubakar Shekau ya bayyana haka

Shugaban kungiyar yan ta’adda na Boko Haram, Abubakar Shekau ya bayyana cikin wani sabon bidiyo inda ya dauki alhakin harin da aka kai a garin Maiduguri a satin data gabata, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Duk da cewa jami’an tsaro sun bayyana samun galaba akan yan Boko Haram din da suka kai harin, tare da kama daya daga cikinsu, Shekau yace suna nan zasu cigaba da yakar kafiran Najeriya.

KU KARANTA: Sojoji sun gudanar da aikin gayya a jihar Legas (Hotuna)

A cikin bidiyon, ya bayyana cewa “Nine Abubakar Shekau, muna yi ma Allah godiya daya kawo mu wannan rana, kuma muna tabbatar ma yan uwanmu cewa mun samu galaba akan sojojin Najeriya.”

Boko Haram ta fitar da sharudɗan yin sulhu da gwamnati

Shekau

Shekau yace indai gwamnati na son yin sulhu dasu, toh lallai sai yan Najeriya gaba daya sun karbi Musulunci kuma sun nemi gafara.

“Rigimar mu daku itace ba kwa bautan Allah yadda ya dace, idan kuka tuba kuka karbi Musulunci, shike nan zamu zuana lafiya daku, kuma zamu ajiye makamai, yaki ya kare.

“Ku sani tsakanin mu daku babu wata maganar yarjejeniya zaman lafiya har sai kun musulunta, daga nan sai mu fara shari’a ta gaskiya.” Inji shi.

Daga karshe, Shekau yace muddin ba haka ba, toh yayansu da jikokinsu zasu gaje su, su cigaba daga inda suka tsaya wajen cigaba da yakar Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel