Dino Melaye zai iya rasa kujerarsa ta majalisa

Dino Melaye zai iya rasa kujerarsa ta majalisa

- A tsarin doka ana iya yi wa dan majalisa kiranye

- Jama'a da yawa a mazabun dan majalisar sun yi rajistar yi masa kiranye

- Idan aka sami kashi 50 suka rattaba hannu, zai dawo gida a sake zabe

A irin dambarwar siyasar da ke gudana a jihar Kogi, inda ake samun rashiun jituwa tsakanin dan majalisa Dino Melaye da gwamnansa Yahaya Bello, an sami wata sabuwar barakar kuma daga mazabar shi Dino Melaye din, inda wasu suke kokarin yi masa kiranye na siyasa.

Muddin dai aka sami isassun kuri'u na saka hannu domin kira ga hukumar zabe ta kwato wa jama'a kujerarsu daga hannun wakilinsu, to dole dan majalisa ya dawo gida a sake zabe a tura wanda jama'a suka yarda da wakilcin sa.

DIno Melaye zai iya rasa kujerarsa ta majalisa

DIno Melaye zai iya rasa kujerarsa ta majalisa

A tsarin dokar zabe dai ana so a sami rabin kuri'u, da guda daya, wato 50% + 1, sa'annan dokar ta fara aiki, inda dole ne dan majalisar ya dawo gida ya zama ba wakili ba kenan. Ba'a taba samun irin hakan ba a tarihin majalisun kasar nan, saboda yawancin talakawa basu ma san suna da wannan damar ba.

A yanzu dai, an sami irin wannan kokari da hakin kai tsakanin jama'ar jihar Kogi ta yamma, inda Dino Melaye ke wakilta, wanda tuni sun yi rajista kuma suna ta saka hannun kada kuri'arsu don yi wa wakilin nasu kiranye.

Rahotanni dai sunce an gano dan majalisar a garuruwan da yake wakilta, inda yaje bada hakuri kuma da rokon ayi masa afuwa a sake bashi dama, amma ance duk da haka gangamin na tafiya ba kakkautawa.

A wasu mazabun ma ance ko sauraronsa ba'a yi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel