‘Yan Boko Haram sun kashe mutane 8 a wani harin bazata

‘Yan Boko Haram sun kashe mutane 8 a wani harin bazata

- Mayakan Boko Haram sun kashe mambobin kunyiyar yan banga guda takwas

- Sun kashe su a wani harin bazata da suka kai kauyen Kayamla dake yankin Konduga

- Wasu mambobin kungiyar ne suka tabbatar da hakan

Mayakan Boko Haram sun kashe mambobin kunyiyar yan banga dake boye suna jiran rundunar soji a cikin bishiya, don gudanar da wani aiki a ranar Lahadi, abokan aikinsu suka fada ma AFP.

A cewar Jaridar The Guardian, Mambobin yan bangan CJTF na jiran sojoji ne a kauyen Kayamla, dake yankin Konduga na jihar Borno, lokacin da harin ya faru.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram ta fitar da sharudɗan yin sulhu da gwamnati

“Mun rasa jarumai takwas a wani harin bazata da mayakan Boko Haram suka kai da misalin karfe 5:30 na safe cewar mamban kungiyar CJTF Ibrahim Liman a babban birnin Maiduguri.

“Yan bangan sun je Kaymala inda rundunar soji zasu hadu da su don kai ma ‘yan Boko Haram hari.

“Abun da basu sani ba, yan ta’addan Boko Haram da suke da masaniya a kan hari, suka kai masu harin bazata ta hanyar haurawa saman bishiyoyin."

Wani dan kungiyar Musa Ari wanda ya taimaka gurin binne jaruman ya mara wa Liman baya a rahoton sa.

Ya ce: "Mun binne wadanda abun ya shafa su takwas. Sojoji ne suka gano gawawwakin su a Kayamla."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel