'Tinubu ne ya sayar mana Buhari a 2015, dole ya fito ya wanke kansa'

'Tinubu ne ya sayar mana Buhari a 2015, dole ya fito ya wanke kansa'

- Bola Tinubu na shan suka tsakanin kabilar Yarabawa kan salon mulkin shugaba Buhari

- Ana shirin fuskantar zabukan fidda gwani a jam'iyyun kasa don 2019

- Adebanjo dattijon kasa ne daga yammacin Najeriya

A shirye shiryen sake duba yiwuwar ko shugaba Buhari na da niyar sake tsayawa takara a zabuka masu zuwa, kuma a yadda ake ganin salon mulkinsa a jam'iyyar APC, bayan shekaru biyu da hawansu mulki, ana ganin za'a sami rabuwar kai ko ma tutsu ga jigo Bola Tinubu muddin ya sake kawo wa yankinsa Buhari don su zabe shi a karo na biyu.

Cif Ayo Adebanjo, shugaban kabilar yarabawa ta Afenifere, yayi baram-barama, inda ya zargi jigo tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu da yi wa kabilar sa zaben tumun dare.

Ya kuma ce dole ne Bola Tinubun ya fito ya wanke kansa kan shirmen da wai ya tafkawa jama'arsa ta tsayar da Buhari a matsayin wanda zasu zaba.

'Tinubu ne ya sayar mana Buhari a 2015, dole ya fito ya wanke kansa'

'Tinubu ne ya sayar mana Buhari a 2015, dole ya fito ya wanke kansa'

Ya kara da cewa, an yi ba'a yi ba ne, wai da sunan dimokuradiyya, domin dai ana jika, babu wani salon dimokuradiyya tare da Buhari, inda yace 'mulkin mutum daya ne kawai ake yi'.

Ya kuma yi kira da a koma tsarin federaliya inda kowanne bangare na hadakar kasa zai ci gashin kansa karkashin gwamnatin tarayya.

Ya kuma ce: 'Tun lokacin da yazo tallar dan takarar jam'iyyar nan Buhari, nace za'a kuma, domin nasan ba wani katabus da Buhari zai iya, na kuma ce kuskure ne a zabe shi, amma aka ki ji na, ai gata nan, shekara biyu ba abun da suka yi sai kara wa kasa kunci da tauyewar arziki.

Ga dukkan alamu dai zata iya chanja zane muddin jam'iyyar APC ta sake tsayar da shugaba Buhari a karo na biyu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel