Rundunar sojin sama ta ƙaddamar da cibiyar ɗinka kayan Soji (Hotuna)

Rundunar sojin sama ta ƙaddamar da cibiyar ɗinka kayan Soji (Hotuna)

- Rundunar mayakan sojin sama ta kasa ta kaddamar wata cibiyar dinke dinke

- Shugaban hafsan sojojin sama, Iya bayis mashal Sadique Abubakar ne ya kaddamar

A kokarinta na inganta ayyukan sojojin ta, rundunar mayakan sojin sama ta kasa ta kaddamar wata cibiyar dinke dinke domin samar da hanyar dinka kayanta ba tare da shigo dasu daga kasashen waje ba.

Dayake jawabi yayin bikin kaddamar da cibiyar dinke dinken a ranar alhamis 8 ga watan Yuni, shugaban hafsoshin rundunar, Iya Mashal Abubakar Siddique ya bayyana farin cikinsa da samar da wannan cibiya.

KU KARANTA: Daruruwan yan Arewa sun fara barin Port Harcourt (HOTUNA)

Abubakar ya bayyana tabbacin dayake da shin a cewa cibiyar zata samar da isassun kayayyakin sojoji akan lokaci kuma cikin sauki da arha, daga nan sai yayi kira ga masu kula da cibiyar dasu tabbata sun sanya idanu wajen ganin an tafiyar da cibiyar yadda ya dace.

Rundunar sojin sama ta ƙaddamar da cibiyar ɗinka kayan Soji (Hotuna)

Cibiyar ɗinka kayan Soji

A nasa jawabin, shugaban sashin kula da cibiyar, Iya bayis Marshal Abubakar Bagare ya bayyana cewar cibiyar na dauke da kayayyakin da suka dace na zamani kamar yadda suke a duk wata cibiyar dinki a fadin duniya.

Rundunar sojin sama ta ƙaddamar da cibiyar ɗinka kayan Soji (Hotuna)

Cibiyar ɗinka kayan Soji

Bagare yace akwai kekunan dinki na zamani guda 86 iri daban daban, sa’annan ya bayyana sun kashe kimanin naira miliyan 40 ne wajen samar da cibiyar gabaki daya, kamar yadda NAIJ.com ta samo rahoto.

Ga suaran hotunan nan:

Rundunar sojin sama ta ƙaddamar da cibiyar ɗinka kayan Soji (Hotuna)

Sadiq Abubakar

Rundunar sojin sama ta ƙaddamar da cibiyar ɗinka kayan Soji (Hotuna)

cibiyar ɗinka kayan Soji

Rundunar sojin sama ta ƙaddamar da cibiyar ɗinka kayan Soji (Hotuna)

Zagayen cibiyar

Rundunar sojin sama ta ƙaddamar da cibiyar ɗinka kayan Soji (Hotuna)

Sadiq

Rundunar sojin sama ta ƙaddamar da cibiyar ɗinka kayan Soji (Hotuna)

Sadiq tare da telolin

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Osinbajo yayi jawabi:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel