'Dole Buhari ya kamo samari da dattijan arewa masu son korar 'yan kabilar Ibo'

'Dole Buhari ya kamo samari da dattijan arewa masu son korar 'yan kabilar Ibo'

- Kungiyar 'yan kabilar Ijaw ta duniya tayi kira ga gwamnatin Buhari ta kaucewa yaki

- An sami baraka tsakanin samarin arewaci da kudancin kasar nan

- 'Halas ne neman 'yancin kai'

Kungiyar samarin kabilar Ijaw ta duniya, wato Ijaw Youth Council, IYC, tayi kira ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da ya gaggauta tsawatarwa wasu samari da dattijan arewacin kasar nan da suka baiwa yabilar Ibo lokacin wa'adi na wata ukku su fice daga yankin arewa, wanda hakan ya jawo tarnaki.

A sanarwar da ta fitar, kungiyar tace babu inda aka haramtawa wasu al'umma neman 'yancin kai daga wata kasa a dokar duniya, don haka babu dalilin da za'a so korar su kabilar Ibo din don kawai suna son balle wa daga Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Daruruwan yan Arewa sun fara barin Port Harcourt (HOTUNA)

'Dole Buhari ya kamo samari da dattian arewa masu son korar 'yan kabilar Ibo'

'Dole Buhari ya kamo samari da dattian arewa masu son korar 'yan kabilar Ibo'

Henry Iyalla, kakakin kungiyar, ya kuma zargi gwamnatin tarayya da shagwaba samarin da dattijan arewar inda yayi kira da a kama su a daure.

A cewar sanarwan: "Kundin tsarin mulki na kasa ya bada dama ga dan kasa da ya je ko'ina yake so ya share guri ya zauna ya kafa kasuwancin sa, ba tare da tsangwama ba, don haka zamu yi kokarin ganin anyi adalci.

"Dole ne mu yi kira ga gwamnatin Buhari da ta yi maza maza ta tare wannan zafin kai tun kafin yaje ya zama wani abu daban."

An dai bada sammacin kame wadanda suka yi wannan sanarwa tun makon jiya, an kuma yi kira da a kame suma dattijan da suka mara musu baya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon hiran Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel