Gwamnatinmu ta jama'a ce - inji wani gwamnan arewa

Gwamnatinmu ta jama'a ce - inji wani gwamnan arewa

- Gwamnan jihar Bauchi ya gana da talakawansa a hanyarsa zuwa gudanar da aiki a yayin da ya ci karo da mutanen

- Gwamnan ya saurari koken mutanen da shawarwarinsu da kuma sauran korafe korafensu

- Gwamnan yana mai ba talakawan uzuri da hakuri tare da basu tabbacin za a gyra

Gwamnan jihar Bauchi Barrista Mohammed A. Abubakar ya tsaya tare da tawagarsa domin ganawa da wasu al’ummar a jihar cikinsu hada guragu yayin da gwamnan ya gana dasu

A ranar mai girma gwamnan ya tsayar da ayarin motocin tare da tawagarsa domin ganawa da talakawansa.

Gwamnan yana kan hanyarsa ne ta zuwa gudanar da aiki a yayin da ya ci karo da mutanen.

Gwamnatinmu ta jama'a ce - inji wani gwamnan arewa

Gwamna M.A Abubakar a lokacin da yake saukowa don ya gana da jama'a

KU KARANTA: Duka kantomomin jihar Bauchi da kansilolinsu sunyi murabus a rana daya

Anyi zaton gwamnan zai wuce ganin cewa galibin mutanen talakawa ne amma matakin da gwamnan ya dauka yayi sabani da haka a inda ya tsaya yaji kokensu da shawarwarinsu da sauran korafe korafensu. Yana mai basu uzuri da hakuri a inda ya saba masu tare da basu tabbacin za a gyra.

Gwamnatinmu ta jama'a ce - inji wani gwamnan arewa

Gwamna M.A Abubakar na gaisawa da wani matashi

Saukin kan gwamnan ya sauyawa al'umomi da dama tunani.

Gwamnatinmu ta jama'a ce - inji wani gwamnan arewa

Gwamna M.A Abubakar na saurari daya daga cikin guragun da ya gana da su

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gaskiyar magana game da rikicin garin Ile-Ife

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel