Kaduna: El-Rufai ya soke dagatai da masu unguwa 390 a Kaduna

Kaduna: El-Rufai ya soke dagatai da masu unguwa 390 a Kaduna

- Gwamna Mallam Nasir El-Rufai ya soke wasu dagatai da masu unguwanni a fadin jihar

- Gwamnati ta dauki wannan matakin ne domin rage nauyin da kirkirar masarautun dagatan ta yi a kan asusun kananan hukumomin jihar

- El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta tuntubi majalisar sarakuna ta jihar kafin dauka matakin soke shugabanin kananan hukumomin

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta soke dagatai da masu unguwanni 390 da aka nada a shekarar 2001.

Wata sanarwar da ofishin gwaman ya wallafa a Twitter ta ce an dauki matakin ne domin rage nauyin da kirkirar masarautun dagatan ta yi a kan asusun kananan hukumomin jihar.

A cewar gwamnan: "Yin garanbawul ga gundumomi da kauyukan zai bai wa kananan hukumomi damar gudanar da manyan ayyuka da ci gaban al'umma".

Kaduna: El-Rufai ya soke dagatai da masu unguwa 390 a Kaduna

Gwamna Mallam Nasir El-Rufai da Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a fadar gwamnatin jihar Kaduna

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, gwamna El-Rufai ya kara da cewa yanzu gwamnatinsa ta dawo da tsarin da aka sani gabanin 2011 na dagatai 77 da masu unguwa 1,429.

Ya ce sun dauki matakin ne bayan da suka tuntubi majalisar sarakuna ta jihar, wacce ta bayar da hoton bayanta.

"Kirkirar mazabu 313 da aka yi daga shekarar 2001 ta kara yawan dagatai zuwa 390, wanda kuma idan aka hada da ma'aikatansu sun zama 2700 kuma kananan hukumomi ne ke biyansu albashi", in ji Gwamna El-Rufai.

KU KARANTA: Sabon salon da Boko Haram ke amfani da shi da watan Ramadana – Kwamishanan labarai

Ya yi kira ga al'umar jihar su goyi bayan matakin da ya dauka saboda hakan zai inganta ayyukan da kananan hukumomi ke gudanarwa.

A cewarsa, "Kamar yadda muka sha fada a baya, an zabi wannan gwamnati ne domin ta dauki matakai masu tsauri amma masu muhimmanci, wadanda za su rage barnar kudi sai dai za su inganta yadda ake gudanar da ayyuka da mulki a kowanne mataki".

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci

na nagari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel