Yakamata al’ummar Igbo su daina kiran Biyafara – Inji wani dan kabilar Igbo

Yakamata al’ummar Igbo su daina kiran Biyafara – Inji wani dan kabilar Igbo

- Wani dan kabilar Igbo ya ce yakamata al’umar Igbo su daina kiran kafa kasar Biyafara

- Wasu ‘yan kabilar Igbo da ‘yan arewa sun ce akwai bukatar daukar matakai dake cike da hikima da hankali domin warware al’amura a cikin ruwan sanyi

- Wasu ‘yan arewa kuma sun koka cewa suna cikin fargaba dare da rana na rashin sani abinda zai iya faruwa

Dangane da dambarwar dake gudana a Najeriya, wace ta hada da batun matasa ‘yan arewa dake cewa ‘yan kabilar Igbo su bar arewacin kasar, ya jawo martani daga bangarori daban daban.

‘Yan arewacin Najeriya, da ‘yan kabilar Igbo dake zaune a kudancin Najeriya, a yankin na kabilar ta Igbo, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da batun lkafa kasar Biyafara da kuma batun da matasan aewacin kasar suka yin a cewa ‘yan kabilar ta Igbo, su bar arewacin Najeriya, nan da watani 3.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, tattaunawar da wasu ‘yan kabilar Igbo da ‘yan arewa ya nuna cewa akwai bukatar daukar matakai dake cike da hikima da hankali domin a samu kaiwa da warware al’amura a cikin ruwan sanyi.

Yakamata al’ummar Igbo su daina kiran Biyafara – Inji wani dan kabilar Igbo

Shugaban 'yan fafutukar kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu

Wani dan kabilar Igbo Cyril Okeke ya ce: “Abinda ke faruwa a yanzu ya isa haka yakamata al’umar Igbo, su daina kiran Biyafara domin samun zaman lafiya, gaskiya mu bamu son ‘yan arewa su bar yankimu haka kuma bamu son ‘yan uwanmu Igbo su bar arewacin Najeriya.”

Shi kuwa Uche, cewa yayi yana goyon bayan cewa duk ‘yan kabilar ta Igbo, dake zaune a arewacin Najeriya, dasu dawo gida yayin da ‘yan arewa su kuma da suke gudanar da harkokinsu a kudanci yankin na kabilar Igbo, su koma yankin sun a arewacin kasar domin acewarsa suna goyon bayan kafar kasar Biyafara.

KU KARANTA: Ra’ayin ‘Yan Najeriya ya sha ban-ban game da korar Inyamurai daga Arewa

Alhaji Musa Saidu shi kuma cewa yayi a wasu wurare da ake furta cewa tilas ne Hausawa su tafi yana tsorata mutane yakamata Igbo, su san cewa Hausawa ma mutane ne.

Shima Alhaji Shehu, cewa yayi suna cikin fargaba dare da rana na rashin sani abinda zai iya faruwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shekaru 50 da fara fafutukar kafa kasar Biyafara, shin 'yan kabilar Igbo za su iya cimma burinsu kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel