Dan sanda ya hallaka dan achaba akan N50

Dan sanda ya hallaka dan achaba akan N50

- Dan sanda ya kashe wani dan babur a kudancin Najeriya

- Idon shaida ya bayyana cewa ya kashe shi ne saboda ya hanashi cin hancin N50

- Amma dan sandan yayi ikirarin cewa ya hallaka shi ne saboda dan babur din yayi kokarin kwace masa bindiga

An hallaka wani dan babur mai suna, Bitrus Chukwudi Ugwuanyi, saboda kin baiwa dan sanda cin hancin N50 a jihar Enugu.

NAIJ.com ta tattaro cewa rikicin ya fara ne tsakanin jami’an yan sanda jihar da yan unguwan Ikpa-modo, Enugu Ezike, karamar hukumar Igboeze North, akan kisan Chukwudi.

Game da cewar jaridan Vanguard, Ugwuanyi ya dauki fasinja a babur dinsa daga Obollo Afor da ke karamar hukumar Udenu zuwa Ogrute inda wani dan sanda ya tsayar da shi a Ugwu Ekposhi kuma ya bukaci N50.

Tashin hankali a jihar Enugu yayinda wani dan sanda ya hallaka dan achaba akan N50

Tashin hankali a jihar Enugu yayinda wani dan sanda ya hallaka dan achaba akan N50

Sai ya fada masa cewa bai da kudi saboda yanzu ya fito aiki, bal wannan ne fasinja na farko da ya dauka.

KU KARANTA: Kalli yada matasa sukaci mutuncin Melaye a Kogi

Game da cewar idon shaida, an harbe Ugwaunyi a gaban fasinjan saboda yaki bayar da kudi N50. Daga baya kuma dan sandan ya bada labarin cewa aid an achaban yayi kokarin kwace masa bindiga ne sai ya kashe sa.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel