An kashe shugaban Boko Haram da wasu da dama yayinda sojojin Najeriya suka kakkabe harin yan ta’addan

An kashe shugaban Boko Haram da wasu da dama yayinda sojojin Najeriya suka kakkabe harin yan ta’addan

- Rundunar operation Lafiya Dole na hukumar sojin Najeriya sun yi nasarar kakkabe wani harin bazata da 'yan Boko Haram suka kai masu

- Sun kashe shugaban 'yan ta'addan na kauyen Jarawa da wasu da dama

- Rundunar sun samo abubuwa da dama daga 'yan ta'addan

Sojojin Najeriya tare da yan banga sunyi nasarar kakkabe harin bazata da yan Boko Haram wanda ya kai ga mutuwar wani shugabna su da kuma wasu yan kungiyar da dama, cewar hukumar sojin Najeriya.

Kakakin sojojin, Sani Usman, ya ce harbe-harben ya dauki tsawon wasu mintuna kusa da kauyen Jarawa a karamar hukumar Kala Balge kafin ‘yan Boko Haram din su tsere.

Usman ya ce: “Rundunar sunyi nasarar kakkabe ‘yan ta’addan Boko Haram da dama ciki harda Abu Nazir, shugaban ‘yan ta’addan a Jarawa.”

An kashe shugaban Boko Haram da wasu da dama yayinda sojojin Najeriya suka kakkabe harin yan ta’addan

An kashe shugaban Boko Haram da wasu da dama yayinda sojojin Najeriya suka kakkabe harin yan ta’addan

Karanta cikakken bayani a kasa:

"Bayan tabbatar da bayanai game da harin da wasu yan ta’addan Boko Haram suka kai kauyen Jarawa, karamar hukumar Kala Balge, jihar Borno, rundunar Bataliya 3 na rundunar Operation LAFIYA DOLE, tare da hadin gwiwar yan bangan JTF a yau Lahadi, 11 ga watan Yuni na 2017, sun yi nasarar kakkabe yan ta’addan Boko Haram.

"Kusan kimanin Kilometre daya zuwa kauyen Jarawa, rundunar sun shiga mummunan harin bazata da ‘yan Boko Haram suka kai, wanda sukayi nasarar kakkabe wa bayan sun dauki tsawon wasu mintuna suna musayar wuta. Sun yi nasarar kora yan ta’addan cikin wani daji dake kusa.

"Rundunar sunyi nasarar kashe ‘yan Boko Haram da dama ciki harda Abu Nazir shugaban yan ta’addan a Jarawa.

An kashe shugaban Boko Haram da wasu da dama yayinda sojojin Najeriya suka kakkabe harin yan ta’addan

Makamai da rundunar ta kwato daga yan ta'addan

"Sun kuma yi nasarar cafke makamai da dama wanda suka hada da bindigar AK-47, bindiga mai ribi biyu guda daya, bam mai karfi da kuma ababen hawa guda uku.

"Bugu da kari sun ceto yara 9 da aka sace sannan ake horar da su a sansanin yan ta’addan dake kauyen."

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon yadda al'umma ke rayuwa a Ohuhu dake jihar Abia

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel