Tunawa da Abiola: Atiku yayi kira ga Shugaban kasa Buhari

Tunawa da Abiola: Atiku yayi kira ga Shugaban kasa Buhari

– Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi magana game da Marigayi Abiola

– Alhaji Atiku Abubakar din yayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari

– Abiola ne dai ya kama hanyar nasara a zaben da aka yi a shekarar 1993

A rana irin ta yau Babangida ya soke zaben Marigayi Abiola

Shekaru 24 kenan yau da faruwar wannan abu a kasar

Wasu Gwamnoni sun bayyana Yau a matsayin ranar hutu

Abiola

12 ga Watan Yuni: Ana Tunawa da Abiola

A Ranar 12 ga Watan Yunin shekarar 1993 aka yi zaben da kusan ya fi kowane inganci a Najeriya. Sai dai wanda ya kama hanyar lashe zaben bai zama shugaban kasa ba, asali ma dai ta kai har Dan siyasan ya mutu a gidan yari.

KU KARANTA: Dangote da wasu sai su yi maganin talauci a Najeriya

Tunawa da Abiola: Atiku yayi kira ga Shugaban kasa Buhari

Alhaji Atiku yayi kira ga Shugaba Buhari

Domin tunawa da wannan rana ne tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar yace ya kamata Gwamnatin Shugaba Buhari ta samu wata makaranta ta sa mata sunan Marigayin wanda gawurtaccen Dan Siyasa ne kuma hamshakin Dan kasuwa.

A Rana irin ta yau ne dai aka shiga cikin wani yanayi a Najeriya shekaru 24 da su ka wuce wanda a cewar babban Dan siyasar Alhaji Atiku daga nan ne aka shirya tubulin siyasar damukaradiyya a Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Allah Sarki Morji Oliaiya ta kwanta dama

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel