Shehu Sani ya ziyarci wani sanannen tsohon dan wasan kwaikwayo na nan arewacin Najeriya (Hotuna)

Shehu Sani ya ziyarci wani sanannen tsohon dan wasan kwaikwayo na nan arewacin Najeriya (Hotuna)

- Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya ziyarci Alhaji Kasimu Yero, Sanannen tsohon dan wasan kwaikwayo

- Sanatan ya ce ya ziyarce shine don ya gode masa saboda gudunmawarsa ga al'adu da zane-zane

- Alhaji Kasimu Yero ya ce babban burinsa yanzu shine ya mayar da dukkanin litattafan labaran Hausa na Magana Jari Ce zuwa salon tsari na fim na Zamani

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani a ranar lahadi, 11 ga watan Yuni ya ziyarci Alhaji Kasimu Yero wani shahararen dan wasan kwaikwayo a shekaru 70s da 80s wanda ake girmamawa a yankin arewacin Najeriya.

Sanata Sani ya ce: “ Na ziyarci Alhaji Kasimu Yero da kuma gode masa saboda gudunmawarsa ga al'adu da zane-zane.”

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari cewa ra’ayoyinsa, iyawa da kuma kwarewarsa wanda ya taimaka ta hanyar kyawawan dabi'u, rayuwa, iyalai da kuma al'umman.

Shehu Sani ya ziyarci wani sanannen tsohon dan wasan kwaikwayo na nan arewacin Najeriya (Hotuna)

Shehu Sani a lokacin da ya ziyarci Alhaji Kasimu Yero

KU KARANTA: Dan majalisar wakilai Honarabul Sani Danlami ya tallafa wa mutane 700 daga mazabarsa Katsina ta tsakiya (Hotuna)

Sanannen tsohon dan wasan kwaikwayo nan na Arewacin Najeriya Alhaji Kasimu Yero, ya bayyana cewar babban burin da yake dashi a yanzu kafin ta Allah ta kasance a kanshi shine, mayar da dukkanin litattafan labaran Hausa na Magana Jari Ce wallafar Marigayi Alhaji Abubakar Imam zuwa salon tsari na fim na Zamani domin kara daukaka darajar Bahaushe a fadin Duniya gaba daya.

Shehu Sani ya ziyarci wani sanannen tsohon dan wasan kwaikwayo na nan arewacin Najeriya (Hotuna)

Shehu Sani na ganawa da sanannen tsohon dan wasan kwaikwayo nan na Arewacin Najeriya Alhaji Kasimu Yero

Dattijo Kasimu Yero ya bayyana hakan ne, lokacin da yake mayar da jawabin godiya ga Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani a yayin wata ziyara da Sanatan ya kai mishi a gidanshi dake unguwar Marafa Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon rikicin kudancin jihar Kaduna kashi na 2

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel