Dan sandan da ya tsira daga fashin banki a Imo na bukatar taimakon miliyan 3 da gaggawa

Dan sandan da ya tsira daga fashin banki a Imo na bukatar taimakon miliyan 3 da gaggawa

- Jami’in dan sandan da ya tsira daga fashin bankin da wasu ‘yan bindiga suka yi a Imo na bukatar miliyon 3 don a yi masa tiyata

- Saje Muran Otu Attang ne kawai ya tsira tasakanin 'yan sanda 3 da suka yi barin wuta da 'yan fashin

- Ga mai son taimaka wa Saje Muran Otu Attang za ku iya amfani da wannan Account Lamba da ke kasa

Wani dan sandan da ya tsira da ransa a wata mumunar fashi da ‘yan bindiga suka yi wa wani banki da ke Imo babban birnin jihar Imo wanda bidiyon harbin ke yawo ta yanar gizo a halin yanzu na bukatar taimako da gaggawa don a masa kwanyar tiyata.

Kamar yadda rahotanni suka ruwaito cewa dan sanda, Saje Muran Otu Attang, shi ne kawai ya tsira tasakanin 'yan sanda uku da suka yi barin wuta da 'yan fashin a lokacin da suka kutsa cikin banki a cikin wani mota mai bakin launin.

Duk da yake biyu daga cikin jami'an 'yan sanda suka mutu, a asibitoci washe garin da al’amarin ya faru, mutumin na cikin wani mummunan halin kamar yadda ya rasa idonsa a lokacin da abin ya faru kuma a halin yanzu yana bukatar tiyata don a cire masa harsasai a kansa.

Dan sandan da ya tsira daga fashin banki a Imo na bukatar taimakon miliyan 3 da gaggawa

Dan sandan da ya tsira daga fashin banki a Imo

KU KARANTA: Hukumar Kwastan ta gano sabuwar dabarar safarar shinkafa

Jami'in dan sandan da ya tsira na da aure da 'ya'ya 3 wanda kuma a halin yanzu yana zama a batcher a Owerri ba tare da wani gabatarwa ba daga ‘yan sandan Najeriya.

Shafin Ifeanyicy.com ta bayyana hakan bayan ziyarar a gidansa a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni. Kamar yadda NAIJ.com ke da labari cewa jami'in dan sandan a halin yanzu yana bukatar miliyan 3 domin yi tiyata.

A halin yanzu jami’in na neman gudunmawar ‘yan Najeriya.

Ga mai son taimaka masa za ku iya amfani da wannan Account Lamba:

ACC NO: 0004096569

NAME: Muran Otu Attang

BANK: Diamond Bank

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai shin 'yan sandan Najeriya abokannin al'umma ne kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel