Kujerar Sanata Melaye na rawa; yace Gwamnan Jihar Kogi ke kokarin ganin bayan sa

Kujerar Sanata Melaye na rawa; yace Gwamnan Jihar Kogi ke kokarin ganin bayan sa

– Gwamnan Kogi ya ware kudi domin ganin a tsige Dino Melaye

– Sanatan Jihar ne yayi wannan ikirari da bakin sa

– Melaye yace Gwamnan ya ware Biliyan guda domin wannan aiki

Yanzu dai Dino Melaye na cikin tsaka mai wuya

Mutanen Yankin san a shirin yi masa kiranye

Sanatan yace Gwamnan ne ke masa wannan kulalliya

Sanata Melaye

Gwamna Bello ke nema ya ga baya na a Majalisa-Inji Sanata Dino Melaye

Har yau dai rikicin Gwaman Yahaya Bello da Sanata Dino Melaye na Jihar Kogi bai kare ba inda kwanan ma Sanatan ya zargi Gwamnan Jihar da hannu a cikin yunkurin da ‘yan mazabar sa ke yi na yi masa kiranye.

KU KARANTA: Mutanen Jonathan sun yi kaca-kaca da shi

Kujerar Sanata Melaye na rawa; yace Gwamnan Jihar Kogi ke kokarin ganin bayan sa

Sanata Melaye da Gwamnan Jihar Kogi

Yanzu dai maganar maido Sanatan gida tayi karfi inda Dino Melaye ya bayyana cewa Gwamna Yahaya Bello ne ya shirya kashe Naira Biliyan guda domin wannan danyen aiki. Sanatan yace ba zai ja da baya wajen fadin gaskiya da nemawa talaka ‘yanci ba.

Kwanakin baya Sanata Melaye da sauran wasu ‘Ya ‘yan Jam’iyyar su ka taso Gwamnan na Kogi a gaba, An nemi Gwamnan ya sauka daga kujerar sa saboda wani zargi. Sai dai Gwamnan yace masu wannan maganar ma dai wasa su ke yi.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dubi yadda mutanen Garin Ohuhu ke rayuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel